Habasha ta toshe shafin Intanet

Masu zanga-zanga a Habasha

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Zanga-zangar Habasha ta yi sanadiyyar mutuwar mutane kusan dari 500

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International, ta fitar da wani rahoto da ke zargin gwamnatin Habasha da toshe hanyoyi ba bisa ka'ida ba, a shafukan sada zumunta da muhawara na Intanet, a wani yunkuri na dakile zanga-zangar adawa da gwamnati, wanda aka kwashe shekara guda ana yi.

Dama dai akwai tsattsauran matakai kan amfani da shafukan intanet a Habasha, tun bayan da aka soma zanga-zangar a watan Nuwambar bara.

Gwamnatin ta kafa dokar ta baci a watan Oktoba, ta kuma zargi 'yan kasan da ke zaune a kasashen waje da ruruta wutar matsalar a shafukan sada zumunta da muhawara, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 500 a kasar.

Wani rahoto da wata cibiyar nazarin manufofi, Brookings da ke Amurka, ya ce Habasha na asarar miliyoyin daloli a duk rana sakamakon rufe shafukan intanet da ke shafar harkokin kasuwanci.

Akalla mutane dubu 11 ne, ciki har da 'yan jarida da manyan 'yan siyasa aka tsare tun bayan da aka kafa dokar ta baci a Habasha.