Nigeria: Ce-ce-kucen da kasafin kudin 2016 ya haifar

A yayin da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke gabatar da kasafin kudin kasar na 2017, mun yi nazari kan irin badakalar da kasafin kasar 2016 ya haifar.

Daga batun beraye, zuwa mafiya, da cushe, kusan za a iya cewa kasafin gwamnatin APC na farko na daya daga cikin abubuwan da suka fi janyo ce-ce-kuce a kasar.

Haruna Shehu Marabar Jos ne ya hada bidiyon.