"Motoci za su riƙa magana da juna a Amurka"

Za a bukaci masu ƙera motoci su inganta fasahar su, ta yadda dukkanin motocin zamani za su iya sadarwa da harshe daya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Za a bukaci masu ƙera motoci su inganta fasahar su, ta yadda dukkanin motocin zamani za su iya sadarwa da harshe daya

Sashen kula da harkokin sufuri na Amurka ya gabatar da wasu dokoki da zasu bukaci dukkanin sabbin motoci su kasance dauke da wata na'ura cikinsu da zata basu damar yin sadarwa da juna.

Jami'ai sunce hakan zai rage kura- kuran da direbobi suke yi, wadanda suke sanadiyyar fiye da kashi 90 cikin 100 na mace- macen da ake samu a hadduran da ake yi akan tituna.

Na'urar zata baiwa motoci damar tura sakonni nuna inda suke, da kuma gudun da mota take, da kuma gano idan akwai wani hadari a gaba.

Za a bukaci masu ƙera motoci su inganta fasahar su, ta yadda dukkanin motocin zamani za su iya sadarwa da harshe daya a lokacin da suke magana da junansu.