Buhari zai gabatar wa Majalisa kasafin kudin 2017

Bayanan bidiyo,

Badakalar da ke kasafin kudin Nigeria na 2016

A ranar Laraba ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai mika wa 'yan majalisar dokokin kasar kudurin kasafin kudi na 2017.

Zai yi hakan ne bayan da majalisar zartarwar kasar ta amince da gabatar da daftarin kasafin kudin a zaman da ta yi ranar 30 ga watan Nuwamba.

Ana sa ran kasafin kudin na badi ya kai fiye da Naira Tiriliyan bakwai.

An dai yi ta fama jerin badakalar yin coge tsakanin 'yan Majalisar dokokin kasar a kasafin kudin 2016.

Sai dai mai magana da yawun Majalisar wakilai Abdurrazak Namdaz ya ce sun ce sun gamsu da yadda aka aiwatar da kasafin kudin kasar na 2016.

A kwanakin baya ne Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya nemi amincewar `yan majalisar dokokin kasar bukatarsa ta karbar rancen dala biliyon 30 daga waje don cike gibin kasafin kudin kasar na shekaru uku masu zuwa.

Shirin rancen dai ya hada da sayar da takardun bashi na kudin Euro da kuma shirin tallafawa kasafin kudi.