Dakarun Syria sun karbo Aleppo daga hannun 'yan tawaye

Baraguzan gini a cikin Aleppo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Birnin Aleppo dai ya kusan zama kufai, saboda yadda yakin ya daidaita shi

A iya cewa wannan ne daddadan labari da 'yan kasar suka samu cikin shekaru hudu da aka kwashe ana gwabza fada tsakanin 'yan tawaye da gwamnatin syria, kafin daga bisani Rasha ta shigo dan taimakawa shugaba Basharul Assad, ba kuma a jima ba sai ga kungiyar IS mai fafutukar kafa daular musulunci ta shigo kasar tare da dagula lissafi.

Jakadan Rasha a majalisar dinkin duniya Vitaly Churkin, yace sojoji za su numfasa, tun da dakarun Syria sun mamaye yankunan da a baya 'yan tawaye da IS ke iko da su.

Ya kuma ce an gama duk wani shiri da ya kamata wanda zai baiwa mayakan 'yan tawaye damar ficewa daga birnin.

Nasarar da aka samu a halin yanzu dai watakil ta yi tasiri matuka da kawo karshen yakin da aka dade ana yi a kasar da ya daidai Syria, da hallaka dubban 'yan kasar, da jikkata wasu da dama, wasu miliyoyi sun rasa muhallansu, ya yin da wasu kuma suka tsere daga kasar.

Wadanda suka makale a yankunan da 'yan tawaye ke iko da su, sun shiga mawuyacin hali, babu abinci da ruwan sha da magani ga marasa lafiyarsu, ga kuma zaman zullumi, da fidda tsammanin sake ingantacciyar rayuwa nan gaba.

Dakarun Syria da na aminiyarta Rasha sun samu nasarar ne saboda takura 'yan tawayen da suka yi a wani dan karamin yanki a arewacin aleppo.

A yanzu dai gundumomin birnin Aleppo irin su Al-Qutayfah, Ras al-Ayn , da Al-Hasakah Al-Rastan da kuma Al-Safira, duk sun dawo hannun dakarun gwamnati. Bangare guda majalisar dinkin duniya da Amurka, sun dora alhakin ta'asar da aka yi a birmin Aleppo akan gwamnatin shugaba Basharul Assad, da Rasha da kuma kasar Iran.