Chelsea ta kara ba da tazara a Premier

Cesc Fabregas na cin Sunderland

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

A duk kungiyoyin Premier Cesc Fabregas ya fi cin Sunderland, inda ya zura musu kwallo biyar

Chelsea ta kara zama daram a kan teburin Premier bayan da ta bi Sunderland gida ta ci ta 1-0, inda ta kara yi wa Arsenal da Liverpool rata da maki shida.

Bayan wasannin na mako na 16 a yanzu Chelsea tana da maki 40, yayin da Arsenal da Liverpool din kowacce take da maki 36.

A karawar tasu a gidan Sunderland wadda take ta karshe, 20, da maki 11, Fàbregas ne ya ci wa Chelsea kwallon daya a minti na 40 da shiga fili.

A sauran wasannin Liverpool ta bi Middlesbrough har gida ta casa ta lallasa da 3-0, Lallana ya fara ci a minti na 29, yayin da Origi ya ci ta biyu a minti 60, kafin kuma minti 8 tsakani Lallana ya kara ta uku. Middlesbrough tana matsayin ta 17 da maki 15.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Kwallo ta biyar da Adam Lallana ya ci a bana, ita ta fara sa Liverpool a gaba

Manchester United ta bi Crystal Palace inda ta ci ta 2-1, a wasan da Paul Pogba ya fara ci ana dab da tafiya hutun rabin lokaci.

Sai kuma McArthur ya rama wa masu masaukin bakin a minti na 66, amma kuma ana dab da tashi ne a minti na 88 sai Ibrahimovic ya kara ta biyu.

Da wannan nasara Manchester United na nan a matsayi na bakwai da maki 27, yayin da Crystal Palace din ta ke ta 16 da maki 15.

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Kwallo tara Ibrahimovic ya ci wa Man United a Premier a bana

Manchester City kuwa karon farko cikin kusan wata uku ta yi nasara a gidanta a gasar ta Premier ta bana, inda ta ci Watford 2-0.

Zabaleta ne ya fara ci wa Manchester City kwallo a minti 33 yayin da Silva ya kara ta biyu a minti na 86.

Manchester City na matsayi na hudu da maki 33, yayin da Watford take matsayin na 11 da maki 21.

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Dan wasan baya na Manchester City Zabaleta ya ci kwallonsa ta farko ta Premier ta bana

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Tottenham a gidanta ta ci Hull City 3-0, inda Eriksen ya ci mata biyu, ta kwallon farko a minti na 14 sannan ya kara ta biyu a minti na 63, yayin da Wanyama ya ci ta uku a minti na 73.

Tottenham din tana nan matsayi na biyar da maki talatin, yayin da Hull City ke matsayi na kusan karshe, 19, da maki 12.

West Brom ma a gidanta ta yi nasarar doke Swansea da ci 3-1, inda Rondón ya yi ta zazzaga wa bakin kwallaye,har uku a cikin minti 13 kacal.

Kwallon farko a minti na 50 sai ta biyu a minti na 61 da kuma ta uku a minti na 63, sai kuma a minti na 78 Routledge ya samarwa Swansean ladan gabenta daya.

West Brom din yanzu tana matsayi na bakwai da maki 23, inda ta kara jefa Swansean cikin hadarin faduwa daga gasar ta Premier, a matsayi na 18 da maki 12.

Stoke City da bakinta 'yan Southampton sun tashi ba ci, amma kuma maki dayan da bakin suka samu ya daga su zuwa mataki na tara, da maki 21 kenan, yayin da Stoke ta dankare a matsayi na 12 da maki 20.