Wata mata ta haihu da mahaifar da aka daskarar tun tana yarinya

Jariri cikin koshin lafiya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Moaza da mijinta Ahmad ba su taba cire tsammani da haihuwa ba

Wata mata ta haihu a London ta hanyar amfani da kwan ta da aka daskarar tun lokacin da ta ke yarinya.

Ana ganin wannan ita ce nasarar da likitoci suka samu yi a karo na farko a duniya, inda aka adana mahaifar da ke dauke da kwayayenta, ta hanyar daskarar da su kafin yarinyar ta soma jinin haila.

Likitocin matar sun ce wannan nasara za ta bai wa sauran wasu mata da suka daskarar da mahaifarsu tun suna yara, kafin soma shan magungunan cutar sankara kwarin gwiwa.

An haifi Moaza Al Matrooshi, mai shekara 24 'yar Dubai, da wata cutar sankara, watau Cancer, wadda ta shafi jini.

Daga bisani aka cire mahaifarta domin soma bayar da magungunan cutar sankarar da ta ke dauke da ita, saboda gudun kar kwayoyin su mata lahani.

Moaza ta ce haihuwar ta zo mata kamar wani abun almara.