An zargi dan siyasa da aikata Luwadi a Malaysia

Sabon sarkin Malaysia, wanda ya yi karatu a Ingila

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

An haramta yin Luwadi a kasar Malaysia

Wata kotu a kasar Malaysia ta yi watsi da karar da tsohon jagoran 'yan adawar kasar Anwar Ibrahim ya daukaka ta karshe, akan samunsa da laifin aikata luwadi.

Hukuncin kotun gwamnatin tarayyar dake a Kuala Lumpur, ta haramtawa Mr Anwar daga tsayawa takara.

Ana kuma ganin hukuncin zai tilastawa dan-siyasar yin zaman gidan yari na akalla wasu karin watanni goma-sha-shida .

A wajen harabar kotun, diyar Mr Anwar, Nurul Izzah, tace zasu cigaba da kokarin ganin an saki mahaifin nata.

Diyar mista Anwar din ta ce sun yi amanna ba shi da laifi, kuma zasu nemi adalci akan barayin gwamnati, kazalika a shirye su ke su cigaba da fafatawa

Ana yiwa Mr Anwar kallon shine babban abokin hamayyar shugaban kasar mai ci Najib Razak, bayan da yayi nasarar cin zabe da ya zo da mamaki a shekarar 2013.

Ya dai nanata cewa zarge- zargen da ake masan, na da nasaba da siyasa.

An haramta yin Luwadi dai a kasar Malaysia, kodayake mutane 'yan kalilan aka taba gurfanawa a kotu game da aikata luwadin.