"A kori Sakataren gwamnatin Nigeria daga aiki"

Rahoton kwamitin Majalisar dattawan Nigeria ya zargi Sakataren gwamnatin da kuma wani kamfaninsa da hannu a badakalar kudaden 'yan gudun hijira.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Rahoton kwamitin Majalisar dattawan Nigeria ya zargi Sakataren gwamnatin da kuma wani kamfaninsa da hannu a badakalar kudaden 'yan gudun hijira.

A Nigeria, Majalisar dattawan kasar ta bukaci shugaba Muhammadu Buhari daya sauke sakataren gwamnatin tarayya Babacir David Lawal daga kan mukaminsa kuma a gurfanar da shi gaban shari'a saboda saba ka'idojin aikin gwamnati.

Majalisar dattawan ta dauki wannan mataki ne bayan ta karbi rahoton wucin gadi na kwamitin da ta kafa don bincike kan zargin karkatar da kudade da kuma kayan agaji da ake turawa 'yan gudun hijirar Boko Haram.

Rahoton kwamitin dai ya zarge Sakataren gwamnatin da kuma wani kamfaninsa da hannu a badakalar.

Sai dai a wata hira da manema labarai, sakataren gwamnatin Babacir David Lawal ya ce zargin da Majalisar ke yi masa tamkar aikin banza ne.