'Yan Nigeria suna jin jiki —Buhari

Asalin hoton, AFP
Shugaba Buhari ya ce an tsara kasafin kudin 2017 ne ta yadda zai tsamo kasar daga cikin halin da ta shiga
Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya ce kusan daukacin al'ummar kasar na jin radadin koma bayan tattalin arzikin da kasar ke ciki a halin yanzu.
Ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da kudurin kasafin kudin shekara mai zuwa a gaban majalisar dokokin kasar.
Sai dai ya ce an tsara kasafin kudin na Naira Tiriliyan bakwai da biliyan 300 ne ta yadda zai tsamo kasar daga cikin halin da ta shiga.
An dai yi ta fama da jerin badakalar yin coge tsakanin 'yan Majalisar dokokin kasar a kasafin kudin 2016.
A kwanakin baya ne kuma Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi amincewar `yan majalisar dokokin bukatarsa ta karbar rancen dala biliyan 30 daga waje don cike gibin kasafin kudin kasar na shekaru uku masu zuwa.
Shirin rancen dai ya hada da sayar da takardun bashi na kudin Euro da kuma shirin tallafawa kasafin kudi.

Buhari ya gabatar wa Majalisa kasafin kudin 2017
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2017 ga 'yan majalisar dokokin kasar ranar Laraba.