Salva Kiir ya bukaci a kawo karhen yakin kasarsa

Salva Kiir

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sudan ta Kudu ta fada yakin ba-sa-sa ne tun bayan sauke Riek Machar daga mukamin mataimakin shuigaban kasa

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir ya yi kira da a gudanar da wata tattaunawa ta kasa domin kawo karshen shekaru ukun da aka shafe ana yakin ba-sa-sa.

Da yake jawabi ga majalisar dokokin kasar, shugaba Kiir ya ce wasu fitattun mutane ne zasu tsara yadda tattaunawar zata kasance ga dukkanin 'yan Sudan ta Kudun.

Ba a dai ambaci sunan abokin hamayyarsa ba, wato tsohon mataimakin shugaban Kasar Riek Machar, wanda ya tsere daga babban birnin kasar bayan rashin nasarar wani yunkuri da aka yi na baya-bayan domin sasantasu, lamarin kuma daya rikide zuwa wani mummunan rikici

Sai dai Afirka ta Kudu tace yana karkashin kulawarta, tana mai musanta rahotannin dake cewa an yi masa daurin talala .

Kwamitin tsaro na MDD ya gudanar da wani zama na musamman akan Sudan ta Kudun a birnin Geneva, inda babbar jami'ar kiyaye hakkin dan Adam Yasmin Sooka, tace nan bada jimawa ba Yakin kabilancin kasar zai kasance babban barazana ga yankin baki-daya