Gwamnonin Nigeria za su daina rayuwar ƙasaita

Gwamnonin Nigeria

Asalin hoton, State house

Bayanan hoto,

Gwamnonin Nigeria na kece raini

Gwamnonin Najeriya sun ce za su rage kudaden da suke kashewa wajen yin rayuwar kasaita sakamakon tabarbarewar tattalin arzikin da kasar ke ciki.

Gwamnanon sun bayyana haka ne a Abuja, babban birnin kasar bayan wani taro da suka yi kan halin da kasar ke ciki.

Gwamnan jihar Kaduna ya shaida wa manema labarai cewa takwarorinsa sun amince su rage yawan kudin da suke kashewa wajen sayen tufafi masu tsada da karbar hayar jirgin sama da yawan motocin da ke jerin-gwanonsu.

Ya kara da cewa, "Bai kamata mu rika gaya wa talakawa ana fama da matsalar tattalin arziki ba amma mu kuma muna ci gaba da kashe kudi a kan abubuwan da ba su da muhimmanci."

A cewar gwamnan na jihar Kaduna, sun gaji matsalar tabarbarewar tattalin arziki ne daga gwamnatin da ta gabata, yana mai cewa fasa bututan man fetur da tsagerun yankin Naija Delta ke yi ya ta'azzara mawuyacin halin da kasar ke ciki.

Da ma dai 'yan kasar na zargin wasu gwamnonin da rashin yi musu ayyukan da suka kamata, inda a maimakon hakan suke yawo a kasashen duniya, kodayake sun musanta zargin.