Jurgen Klopp ya kare Karius

Jurgen Klopp

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Jurgen Klopp ya ce: ''Ba wai ina son in ce Karius ba shi da matsala ba ne''

Kocin Liverpool Jurgen Kloop ya kare mai tsaron ragar kungiyar Loris Karius da cewa, nan gaba kungiyar za ta ci moriyarsa sosai, duk da rashin sa shi a wasan da suka ci Middlesbrough 3-0.

Simon Mignolet ne ya maye gurbin golan mai shekara 23, wanda masu sharhin wasanni ciki har da tsoffin 'yan wasan Manchester United Gary da Phil Neville suka yi ta sukar shi, kan kurakuren da ya yi a wasansu da West Ham da Bournemouth.

Klopp ya ce: "Ni ba ni da wata sha'awa kan wani matsin-lamba daga jama'a, abin da na damu da shi kawai, shi ne yaron. Ban ga dalilin da zai sa a yi ta caccakarsa ba a kan abin, ya karaya.''

Kocin dan Jamus ya kara da cewa: "Karius yana da abubuwan da masu tsaron raga da yawa za su so a ce suna da su.

Muna son mu raya 'yan wasa ne, su zama gwanaye- amma fa ba wai muna son mu shawo kan mutane cewa wai ba shi da matsala ba ne.

"Na san shi sosai, kuma ya fi yadda yake a wasanni biyu na baya. Lamari ne da Liverpool za ta ci moriya a gaba.''

Klopp ya sayo Karius daga tsohuwar kungiyarsa Mainz a kan fan miliyan 4.7 a lokacin bazara, kuma Bajamushen ya yi wasa 10 na Premier, ba a ci shi ba a uku daga ciki.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

''Karius matashin gola ne da zai farfado'' in ji Klopp

Sai dai kuskuren da ya yi a kwallon da Bournemouth ta ci su a kusan karshen wasansu na ranar 4 ga watan Disamba, ya jawo masa suka da kalamai daga Gary Neville.

Yayin da tsohon dan wasan baya na Liverpool Jamie Carragher ya ce har yanzu golan yana da bukatar horo sosai.