Kofin Duniya: An yi watsi da shirin Fifa na kara kasashe

Shugaban ECA Karl-Heinz Rummenigge

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugaban hadakar Karl-Heinz Rummenigge ya buga wa Jamus ta Yamma wasa lokacin da suka zo na biyu a gasar kofin duniya ta 1982 da 1986

Hadakar manyan kungiyoyin kwallon kafa na Turai ta yi watsi da shirin shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, Gianni Infantino, na kara yawan kasashen gasar cin kofin duniya da za a yi a 2026, daga 32 zuwa 48.

Shugaban hadakar, ko kungiyar ta ECA, tsohon dan wasan Jamus Karl-Heinz Rummenigge, ya ce duk wani abu da za a yi a game da gasar kamata ya yi, a mayar da hankali kan wasan.

Amma ba siyasa ko kasuwanci ba, don haka bai kamata a kara yawan masu shiga gasar ba.

Kungiyar ta ce daman tuni yawan wasan da ake yi a shekara ya yi yawan da ba za a amince da shi ba.

A farkon watan nan ne shugaban na Fifa, ya gabatar da shawarar mayar da gasar ta duniya ta kunshi kasashe 48, da za a raba zuwa rukuni 16, kowanne da kasashe uku-uku.

A ranar 9 ga watan Janairu ne majalisar zartarwar Fifa, za ta tattauna kan shirin na Infantino.

Shugaban na Fifa ya yi alkawarin kara yawan kasashen gasar ne, a lokacin yakin neman zabensa, domin a cewarsa yana son ba wa karin kasashe damar shiga gasar.

A shekara ta 1998 ne aka kara yawan kasashen gasar daga 24 zuwa 32, amma kuma duk wani kari da za a sake yi yanza da wuya ya fara aiki kafin gasar ta 2026.

Hadakar kungiyoyin kwallon kafar na Turai, ta kunshi kungiyoyi ne sama da 200 da suka hada da Real Madrid da Barcelona da Juventus da Bayern Munich da Manchester United da Chelsea.