An soki gwamnatin DRC kan soke gasar kwallon kafa

Moise Katumbi shugaban TP Mazembe
Bayanan hoto,

Moise Katumbi na kalubalantar Shugaba Kabila a zaben kasar da aka dage

Shugaban TP Mazembe, Zakarun gasar lig din Jamhuriyar Dumokradiyyar Congo Moise Katumbi, ya yi Alla-wadai da matakin gwamnatin kasar na dakatar da gasar lig da sauran wasannin kwallon kafa a kasar har sai abin da hali ya yi.

Katumbi wanda ke kalubalantar Shugaba Joseph Kabila a zaben kasar da aka dage, ya sheda wa BBC cewa, wasan kwallon kafa shi kadai ne abin da a yanzu yake nishadantar da jama'a a kasar

Sannan kuma ya soki matakin, saboda yana ganin ba ta yadda tawagar kwallon kasar za ta iya shirya tunkurar gasar cin kofin kasashen Afrika da za a fara a wata mai zuwa a Gabon, ba tare da 'yan wasan suna buga wata gasa ba.

A ranar Laraba ne gwamnatin ta DRC ta dakatar da babbar gasar lig din kwallon kafar da sauran harkokin wasannin kwallon kafa, saboda tana fargaba rikici ka iya tashi a filin wasa ganin irin zaman dar-dar da ake a kasar.