Za mu dauki fansa a kan Russia — Obama

Zuwan Barack Obama Laos

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Barack Obama ya ce shugabancin Amurka bai kamaci 'sakarai'.

Shugaban Amurka, Barack Obama ya ce Amurka za ta mayar wa da Rasha martani kan kutsen bayanai lokacin zaben kasar.

An dai zargi Rasha da kutsen bayanai ga tarin imail na 'yar takarar jam'iyyar Democrat, Hillary Clinton.

Sannan kuma an zargi Rashar da hannu wajen nasarar da Donald Trump ya samu a zaben shugaban kasar.

Obama ya ce "babu shakka daukar mataki a kan dukkan kasar da ta yi kokarin shigar wa Amurka hanci da kudundune musamman kan abin da ya shafi zabenta."

Ya kara da cewa Amurka za ta yi wannan ramuwar gayyar ne a lokacin da ta ga ya dace, a inda kuma ya ce wasu matakan za a dauke su a bainar jama'a wasu kuwa a boye za a dauka.

Sharhi, Usman Minjibir

Alaka tsakanin Amurka da Rasha dai ta kara yin tsami ne tun bayan da shugaban Amurkar mai jiran gado, Donald Trump, ya bayyana shugaban Rasha, Vladimir Putin da wanda ya fi Obama kwarjini.

Sannan kuma mista Trump ya yi alwashin dinke barakar da ke tsakanin Amurkawa da Rashawa da suka dade ba sa jituwa.

Ko da rikicin da ake yi a gabas ta tsakiya Rashar da Amurka sun ja daga musamman a Syria.

Yayin da Amurka ke goyon bayan 'yan tawaye, Rasha kuwa tana marawa gwamnatin Bashir al-Asad ne.

Har wayau, kasashen biyu sun dauki tsagi a rikicin siyasa tsakanin Saudiyya da Iran, a inda America ke goyon bayan Saudiyya, ita kuma Iran tana samun kulawar Rasha.