'An sake samun wasu alkalai da cin hanci a Nigeria'

Walter Onnoghen

Asalin hoton, NIGERIAN GOVERNMENT

Bayanan hoto,

Walter Onnoghen ya ce ba zai bari a ci gaba da bata wa alkalai suna ba

Hukumar da ke sanya ido a fannin shari'ar Najeriya ta bukaci a kori wasu alkali biyu daga aiki bisa zargin da ta yi musu na karbar hanci.

Wata sanarwa da kakakin hukumar Soji Oye ya fitar ranar Juma'a ta bukaci a kori mai shari'a Ugbo Ononogbo na babbar kotun jihar Abia, sannan a yi wa mai shari'a Nasir Gummi na babbar kotun jihar Zamfara ritayar dole ba tare da bata lokaci ba.

Mr Oye ya kara da cewa, "Hukumar da ke sanya ido kan fannin shari'a karkashin jagorancin alkalin alkalai na kasa mai shari'a Walter S. N. Onnoghen, a taron da ta yi na 80, ta nemi gwamnan Abia ya kori Ugbo Ononogbo, yayin da ta yi kira ga gwamnan Zamfara da ya yi wa mai shari'a Gummi ritayar dole saboda samunsu da cin hanci."

Sai dai alkalan ba su ce komai a kan zargin da ake yi musu ba.

Hukumar ta kuma gargadi wasu alkalai, cikin su har da D. O. Oluwayemi na ma'aikatar shari'a ta jihar Lagos da mai shari'a M. A. Savage na babbar kotun Lagos kan zargin aikata ba daidai ba.

A watannin baya bayan nan dai bangaren shari'a na Najeriya na shan caccaka daga 'yan Najeriya, musamman bisa zargin cin hanci da rashawa da ake yi wa alkalai.

Tuni dai aka gurfanar da wasu alkalan a gaban kotu bayan hukumar tsaro ta farin-kaya ta kai samame gidajensu, inda ta ce ta samu makudan kudaden da ake zargin sun karba ta hanyar cin hanci.