An zargi Kamaru da take hakkin 'yan jarida

Wani jami'in tsaro

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ana zargin jami'an tsaron Kamaru da tauye hakkin 'yan jarida

Kungiyar da ke kare hakkin 'yan jarida ta Committee to Protect Journalists ta zargi gwamnati da jami'an tsaron Kamaru da murkushe 'yan jarida.

CPJ ta ce a makonni kadan da suka wuce, an kama 'yan jaridar da ke daukar labaran zanga-zangar da aka yi a kasar, sannan an dakatar ko rufe wasu gidajen rediyo da talabijin da kuma jaridu.

Kungiyar ta bayar da misali kan dan jaridar gidan rediyon Faransa Ahmed Abba, wanda gwamnatin kasar ke ci gaba da tsarewa tun watanni 16 da aka kama shi, inda yake jiran shari'a a wata kotun soja.

Ana zarginsa da taimakawa 'yan kungiyar Boko Haram, kodayake ya sha musanta zargin.

Har yanzu dai gwamnatin Kamaru ba ta ce komai a kan wadannan zarge-zarge na CPJ ba.