Dan 12 ya nemi tayar da bam a Jamus

Kasuwar sayen kayan bikin Kirisimeti da ke garin Ludwigshafen a Jamus

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Yaro dan shekara 12, ya nemi ya tayar da bam a wata kasuwar sayen kayan bikin Kirisimeti da ke garin Ludwigshafen a Jamus

Masu shigar da kara sun ce wani yaro dan shekara 12, mazaunin Jamus kuma dan asalin kasar Iraki, ya nemi ya tayar da bam a wata kasuwar sayen kayan bikin Kirisimeti da ke garin Ludwigshafen, a Jamus.

Yaron ya ajiye wata jaka da ke dauke da ababen fashewar da basu yi nasarar tashi ba a watan Nuwamba, inda ya kuma sake dasa wasu a wani dakin taro bayan 'yan kwanaki kadan.

Amma kuma sai wani mazaunin garin da ya lura da shi, kuma ya ankarar da 'yan sanda, amma babu wanda ya samu rauni.

Yaron, mai shekaru 12 yanzu yana hannun jami'an tsaro, kuma ana tunanin cewa an cusa masa tsattsaurar ra'ayin addinin musulinci ne daga kungiyar IS.

Mujallar Focus ta ambato jami'an tsaro da masu shigar da kara na cewa yaron na da tsattsaurar ra'ayi, kuma akwai alamun cewa yana bin umurnin wani dan kungiyar IS, amma ba a tabbatar ba.

Ofishin shigar da kara a Jamus, bata tanka ba game da batun ko lamarin na da wata alaka da kungiyar IS, amma ta tabbatar da cewa ana gudanar da bincike.