MMM: Anya masu jari zasu samu kudadensu?

Asalin hoton, MMM Nigeria
Shafin tsarin zuba jari na MMM ya samu tsaiko a Najeriya
Tsarin MMM mai rubanya riba, da ya zamo kamar wutar daji a Najeriya, ya samu tsaikon da ya bar masu hannun jari a cikin tashin hankali, game da makomar kudaden su.
Tsarin MMM din dai, ya dore ne daga hadin kan jama'a, domin taimakawa juna.
Ya kamata masu hada-hadar MMM din su samu kashi 30 cikin dari na jarin da suka zuba.
An kuma kaddamar da tsarin ne a Najeriya a watan Nuwambar 2015, kuma masu gudanar da tsarin sun ce suna da mutane miliyan uku da suka zuba jari a ciki.
Amma kuma akwai abubuwa marasa dadin ji a tarihin tsarin MMM.
Asali ya samu tushe ne a Rasha a shekarun 1990, inda rugujewar sa bayan wasu 'yan shekaru ya yi sanadiyyar asarar akalla dala miliyan 100 na kudin masu zuba jari.
Gwamnatin Rasha dai ta haramta wannan tsarin a kasar, kuma ta rufe wanda ya kirkiro da ita a gidan kaso har tsawon shekaru hudu.