MDD ta soki gwamnatin Aung San Suu Kyi

Sojojin Myanmar ko kuma Burma

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Ana zargin sojoji da take hakkin bil adama a Rohingya

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kakkausar suka ga gwamnatin Myanmar, wadda Aung San Suu Kyi ke jagoranta, saboda abinda gwamnatin ke yi wa al'umar yankin Rohingya, marasa rinjaye.

Ofishin kare hakkin bil Adama na Majalisar Dinkin Duniyar, ya ce yana samun rahotanni na fyade, da kashe-kashe da sauran ayyukan keta hakkin bil adama.

Shugaban Kare hakkin bil Adama na Majalisar Dinkin Duniya, Zeid Ra'ad al Hussein, ya ce dabarar da gwamnatin Myanmar ke amfani da ita, ba ta alheri ba ce, kuma keta ce.

Musulmi 'yan kabilar Rohingya akalla 77 ne aka kashe, kuma aka tilasta wasu sama da dubu 25 tserewa, saboda samamen da sojoji ke kai wa a jihar Rakhane ta Myanmar.