"Na kashe mutane uku”- Duterte

Shugaban Philipines Rodrigo Duterte

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Shugaba Duterte ya ce yana kisa ne domin ya burge abokai, kuma domin ya nuna shi ma yana iya aikata kisa.

Shugaban Philipines Rodrigo Duterte ya tabbatar wa da BBC cewa ya harbe mutane uku har lahira, a lokacin da ya ke magajkin garin Davao a kasar.

Duterte ya ce, "Na kashesu su ukku...ban san adadin harsashen dana na harba ba a jikin su ba. Ya dai faru kawai, kuma ba zan iya karyatawa ba."

Wannan furucin na sa na zuwa ne sa'o'i kalilan bayan da kakakin gwamnatin kasar ya fito ya musanata zargin cewa shugaban ya taba aikata laifin kisa.

Takaddamar ta tashi ne tun ranar Laraba, a fadar shugaban kasar, inda ya shaida wa manema labarai cewa ya taba aikata kisa a baya.

Ya ce yana yi ne domin ya burge abokai, kuma domin ya nuna shi ma yana iya aikata kisa.

Shugaban ya ce, "Ina zagayawa akan babur dina, in rika kai wa in kawo a kan tituna, kawai domin neman tsokana. Kawai kuma domin neman wanda za mu yi fito na fito da shi ne domin na samu dalilin kashe shi."

Mista Duterte dai ya yi magajin garin Davao ne da ke kudancin kasar, har wa'adin shekara goma, inda ya yi suna wajen yin amfani da mugunta wajen hana aikata laifuka da kuma tura 'yan ina-da-kisa domin kashe jama'a.