Nigeria: An karya ka'ida wajen ginin cocin da ya rufta

Wani gini da ya rufta

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Majami'ar da ta ruguje a ranar Asabar, ta kashe mutane da dama a birnin Uyo da ke jihar Akwa Ibom.

Hukumomi a Najeriya sun ce bincike ya nuna cewa akwai kurakurai a tsarin ginin, wata majami'a da ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama a birnin Uyo da ke jihar Akwa Ibom, sakamakon rugujewar da ta yi.

An ce ba a bi tsarin doka ba wajen gina cocin wadda ta ruguje ranar Asabar din da ta gabata.

Hukumar ta kula da ayyukan gine-gine a Najeriya, ta ce ba ta bayar da izinin gina cocin ba, kuma hukumomi sun sha bayar da umarnin dakatar da ginin, amma sai aka yi biris, a karshe kuma ginin ya rufta tare da manyan karafa, a kan masu ibada.

Hukumar ta yi kira ga injiniyoyin da ke da hannu a ciki, da su mika kansu ga 'yan sanda.

Ana dai yawan samun rushewar gine-gine a Najeriya saboda rashin ingancinsu da kuma kayakin aiki marasa inganci.