Syria: An dakatar da fitar da fararen hula a Aleppo

Yarjejeniyar tsagaita wuta ta rushe a Aleppo

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

An dakatar da fitar da fararen hula daga Aleppo

Tun daga safiyar ranar Juma'a, babu motocin kwashe mutane daga birnin Aleppo, lamarin da ya janyo matukar damuwa game da halin da dubban fararen hula, wadanda aka yi imanin suna makale a matatarrar 'yan tawaye, ke ciki.

An dai dakatar da kwashe mutanen ne bayan da mayaka, masu goyon bayan gwamnati suka ce dole a aiwatar da wata yarejeniya ta bani-gishiri-in-baka-manda,

An kwashe wasu mutanen da aka jikkata a wasu kauyuka biyu da 'yantawaye suka yi wa kawanya ma.

Dukkan bangarori dai sun zargi juna da keta sharuddan yarjejeniyar da aka kulla ta dakatar da bude wuta.