Da bakin cikin Syria nake kwana — Obama

Obama ya bayyana takaicin rashin yin katabus kan rikicin Syria

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

A watan Janairu Obama zai mika mulki ga Donald Trump

Shugaban Amurka mai barin gado, Barack Obama, ya ce a kullum yana barci ya tashi da takaicin rikicin Syria, a ransa.

A wani taron manema labarai na karshe da ya yi a matsayinsa na shugaban Amurka, Obama ya ce ya yi duk iya bakin kokarinsa wajen Amurka ta shiga tsakani.

Ya kara da cewa ya kamata ace Amurkar ta aike da dakarunta zuwa Syria ko da kuwa Majalisar Dokokin Amurka ba ta amince ba.

Tundai shekarar 2011 ne rikici ya barke tsakanin gwamnati da 'yan tawaye da manufar kawar da shugaban.

Hakan ya haddasa mutuwar dubban mutane da kuma tilastawa miliyoyi yin hijra.