China ta dauke jirgin Amurka maras matuki

China da Amurka na zaman 'yan marina

Asalin hoton, Vincent Yu

Bayanan hoto,

Xi Jinping

Amurka ta ce ba ta ji dadin dauke wani jirgi maras matukinta da ke shawagi a karkashin ruwa da sojin ruwan China suka yi ba, a tekun kudancin Chinar.

Hedikwatar tsaron Amurkar, Pentagon ta ce jirgin maras matuki na shawagi lokacin da sojojin ruwan na China suka yi awon gaba da shi.

Har yanzu dai China ta yi gum, ba ta ce uffan ba kan wannan ikrari.

Daman dai Amurkar ita ma ta batawa Chinar rai, a lokacin da shugaban Amurka mai jiran gado, Donald Trump, ya yi magana da shugabar Taiwan.

Al'amarin ya sanya China tunanin ko Amurkar na son taimaka wa Taiwan din ne samun 'yancin cin gashin kai.