Zan tsaya takarar shugabancin Korea ta Kudu

Asalin hoton, AFP
A karshe watan Disamba Ban-Ki Moon zai sauka dag kujerar MDD
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon, ya ce zai tsaya takarar shugabancin Korea ta Kudu, da zarar wa'adinsa na MDD ya cika a karshen wannan watan.
A wani taron manema labarai na karshe da ya yi a matsayin shugaban MDD, mista Ban ya ce zai koma kasar tasa domin tallafa mata ta hanyar da ta dace.
A watan Disambar 2017 ne ake sa ran gudanar da babban zaben Korea ta Kudun.
Sai dai kuma za a iya gudanar da zabe nan da kwanaki sittin.
Ana jiran kotun tsarin mulkin kasar ta yanke hukuncin tsige shugaba Park Geun-Hye wadda aka samu da hannu a badakalar rashawa da cin hanci.