Mugabe ne dan takararmu a 2018—ZANU-PF

Robert Mugabe

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shekarun shugaba Robert Mugabe 92

Jam'iyyar ZANU-PF mai mulki a Zimbabwe ta tabbatar da shugaban kasar Robert Mugabe a matsayin dan takararta a zaben 2018.

Mugabe mai shekaru casa'in da biyu, ya kasance akan mulki tun da kasar da samu 'yan cin kai a 1980.

A wajen babban taron ta a Masvingo, reshen matasa na jam'iyyar ta ZANU-PF ya ce kamata ya yi ma a bayyana Mista Mugabe a matsayin shugaban kasa na iya rayuwarsa.

Sai dai Mista Mugabe ya fuskanci manya-manyan zanga-zanga a wannan shekara, inda wasu mutanen kasar da dama ke nuna damuwa kan tabarbarewar tattalin arzikin kasar, da kuma irin shugabancin sa.

Wani bangare na jam'iyyar Mista Mugaben ma yana adawa da shi, saboda yana so ya gaje shi bayan ya sauka daga mulki.