An kasa samun daidaito yayin da wa'adin Kabila ke cika

Asalin hoton, Getty Images
Masu zanga-zangar neman Shugaba Joseph Kabila ya sauka
Hadakar jam'iyyu da bangaren 'yan adawa a jamhoriyar Dimukradiyar Congo, sun kasa cimma yarjejeniya a wani zama na gaggawa da suka yi gabanin karewar wa'adin shugaba Joseph Kabila a ranar Litinin mai zuwa.
An dage zabukan kasar, sannan 'yan adawa a kasar sun sha alwashin yin zanga-zanga kan abin da suka kira yunkurin shugaba Kabila na kin sauka daga mulki.
An tsaurara matakan tsaro a birane da dama a fadin kasar.
Akalla mutane hamsin ne suka mutu a zanga-zangar da aka yi a Kinshasa, babban birnin kasar a watan Satumba.
A ranar Laraba ce za a ci gaba da tattaunawar, wacce cocin katolika ke shiga tsakani.