'Yan adawa a Niger sun nemi Issoufou yi murabus.

Zai bar mulkin kasar a 2012
Bayanan hoto,

Mahamadou Issoufou ya ci zabe a 2016

Kawancen jam'iyun siyasa na FRDDR a jamhuriyar, ya yi kira ga shugaban kasar, Mahamadou Issoufou da ya yi murabus daga mukaminsa.

'Yan adawar dai na zargin shugaban ne da kasawa da rashin iya mulki.

Sun kuma ce tunda shugaban ya hau mulki a 2016, kasar ta fada cikin halin kaka ni ka yi.

Sai dai shugaba Mahamadou Issoufou, ya ce yana nan kan kujerarsa ta mulki sai 2021, inda yake fatan mika mulkin ga sabon zababben shugaban kasar.