'Mun bai wa Majalisa mako biyu ta tabbatar da Magu'

Sanatoci

Asalin hoton, NIGERIA SENATE

Bayanan hoto,

Ana zargin sanatoci da dama da cin hanci

Wasu 'yan Najeriya sun bai wa 'yan majalisar dattawan kasar wa'adin mako biyu da su tabbatar da Ibrahim Magu, a matsayin shugaban hukumar EFCC ko kuma su yi zanga-zanga a mazabun 'yan majalisar.

Sun bayyana hakan a wani taron manema labarai da suka gudanar a birnin Legas.

Sun kara da cewa duk wani yunkurin hana tabbatar da Ibrahim Magu a matsayin shugaban EFCC na dindindin zai iya yin zagon-kasa a yakin da Shugaba Muhammadu Buhari ke yi da cin hanci da rashawa.

A makon da ya gabata ne dai 'yan majalisar ta dattawan suka ki tabbatar da Magu a matsayin shugaban EFCC.

Sun ce sun yi hakan ne saboda rahoton sirri da suka samu a kansa na aikata ba daidai ba.

Sai dai shugaban na EFCC bai ce komai kan batun ba.

Shugaban masu rinjaye na majalisar Sanata Mohammed Ali Ndume ya shaida wa BBC cewa sun mika wa Shugaba Buhari rahoton, yana mai cewa suna jiran matakin da zai dauka kafin su yi yunkuri na gaba a kan Ibrahim Magu.

Wasu dai na zargin cewa takun-sakar da ake yi tsakanin hukumar tsaro ta DSS da EFCC ce ta sanya manyan jam'ian na DSS suke yi wa Ibrahim Magu bi-ta-da-kulli, kodayake ba su ce komai a kan zargin ba.