Rohingya: An hana zanga-zanga a Bangladesh

Bangladesh

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan sanda sun ce mutane dubu 6 ne suka shirya wa zanga-zangar

'Yan sanda a Dhaka babban birnin Bangladesh, sun hana dubban masu zanga-zanga yin tattaki zuwa iyakar kasar da Myanmar, don nuna kin jinin dirar mikiyar da ake yi wa Musulman Rohingya marasa rinjaye.

Wani babban jami'in 'yan sanda ya ce mutane kimanin dubu shida, 'yan jam'iyyar Musulunci ne suka shirya yin tattakin, suna masu furta kamalai na yin Allah wadai da shugabar Myanmar Aung San Suu Kyi.

Bude wuta kan 'yan kabilar Rohingya da sojojin Myanmar suka yi a kwanakin baya, ya tilasta wa dubban 'yan kabilar guduwa zuwa tsallaken iyakar.

Sai dai hukumomin Bangladesh din, sun tsananta fatirin ne a kan iyakar, tare da mayar da 'yan gudun hijirar inda suka fito.