Nigeria: 'Abin da ke haddasa rikicin Fulani da Tibi a Taraba'

Rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma ya zama ruwan dare a arewacin Najeriya
Bayanan hoto,

Fulani dai na fama da tashe-tashen hankali da sauran kabilu

Rundunar 'yan sanda jihar Taraba a Najeriya, ta ce dalilai uku ne ke janyo rikici tsakanin kabilar Fulani da Tibi a jihar.

A karshen mako ne mutane shida suka mutu a kauyen Sabon Gida, a garin Dan Anacha na jihar sakamakon wani rikici da ya barke tsakanin Fulani da Tibin.

Dangane kuma da rahotannin da ke cewa mutanen kauyen sun gudu, mista Yakubu ya ce ba haka ba ne illa dai sun koma cikin birni.

Ko a watan Fabrairu ma irin wannan rikicin ya afku a jihar, al'amarin da ya yi sanadiyyar mutuwa da jikkatar mutane da dama.

Kwamishinan 'yan sanda jihar, Yunana Yakubu Babas wanda ya je wurin da rikicin ya faru, ya ce ya zauna da duk masu fada aji a garin kuma sun zayyana masa dalilai uku da ke haddasa rikicin.

Fulani sun ce ana kashe musu mutane da dabbobi

Gwamnati ba ta dauki mataki ba duk kuwa da kwamitocin da ake kafawa

Wani nadin sarauta da aka yi wa 'yan kabilar Tibi ba bisa ka'ida ba wanda kuma yake kawo rashin jituwa tsakaninsu da baki

Mista Yakubu ya ce zai iya yinsa wajen ganin ba a sake samun afkuwar irin wannan rikicin ba a nan gaba.