Joseph Kabila na son yin tazarce ba tare da zabe ba

Akwai yiwuwar barkewar zanga-zanga a kasar

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Joseph Kabila na son tazarce ba tare da zabe ba

Ana zaman dar-dar a jamhuriyar Dimokradiyyar Congo bisa tsoron barkewar sabon rikici a ranar Litinin, ranar da wa'adin shugaban kasar, Joseph Kabila yake karewa.

An dai tashi baram-baram daga tattaunawa tsakanin bangaren gwamnati da jam'iyyun adawa, bayan da shugaba Kabila, ya nemi ya zarce da mulkin kasar tunda dai ba a yi zaben da zai ba wa wani ikon karbar sa ba.

Ana tsammanin cewa za a iya samun barkewar zanga-zanga a ranar Litinin din daga bangaren jam'iyyun adawar kasar bisa abin da suka kira shirin shugaba Kabila na cigaba da mulki.

A daren Lahadi ne aka kakkafa wuraren bincike na sojoji da 'yan sanda a ciki da wajen babban birnin kasar, Kinshasa.

Kuma gwamnati ta ce za ta toshe kafafen sadarwa na sada zumunta da kuma yin dirar mikiya kan masu zanga-zanga.

A watan Satumbar da ya gabata dai an kashe masu zanga-zanga fiye da 50, a kasar.

Tun dai shekarar 2001 Mista Kabila yake mulki a kasar.

Ya hau mulkin ne kwanaki goma bayan kisan gillar da aka yi wa mahaifinsa, shugaba Laurent-Désiré Kabila.