Dan bindiga ya harbe jakadan Rasha a Turkiyya

Jakadan Rasha a Turkiyya Andrei Karlov

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Andrei Karlov na ziyartar wurin baje kolin kayan zane-zane ne a babban birnin kasar

Wani dan bindiga ya kashe Jakadan Rasha a Turkiyya, Andrei Karlov, a yayin wata ziyara da ya kai wani dakin baje kolin zane-zane da ke Ankara babban birnin kasar.

Mutane da dama sun samu raunuka a lamarin, wanda ya afku kwana daya bayan wata zanga-zangar adawa da aka yi a Turkiyya kan rawar da Rasha ke takawa a Syria.

Gidan talabijin din Rasha ya ce jakadan ya ziyarci wani wurin baje kolin kayan zane ne da aka yi wa lakabi da "Russia as seen by Turks".

'Yan sanda sun ce an kama dan bindigar, amma kuma ba su bayar da karin bayani ba game da lamarin.

An dai garzaya da Mista Karlov zuwa asibiti cikin gaggawa, inda daga bisani aka tabbatar da cewa ya mutu.

A kwanakin baya-bayan nan Rasha da Turkiyya sun yi aiki tare domin samar da yarjejeniyar tsagaita wuta a birnin Aleppo.