Syria: An kwashe dubban mutane daga Aleppo

Yankin Aleppo da ke fama da rikici a Syria

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Ana fatan cewa yarjejejiyar kwashe mutanen za ta dore

Dubban mutane ciki har da marayu aka kawashe daga birnin Aleppo, yankin da ke fama da rikici a kasar Syria.

A ranar Litinin ne mutane fiye da 4,500 suka bar yankunan gabashin birnin da ke hannun 'yan tawaye.

Bana Alabed 'yar shekera bakwai, na daya daga cikin mutanen, kuma ta rika yin amfani da shafin Twitter wajen bayyana halin da suka samu kansu a cikin.

A daya bangaren kuma, an soma fitar da jama'a daga wasu yankunan Idlib, inda gwamnatin Syria ke da iko da safiyar ranar Litinin.

A yayin da ake ci gaba da fitar da mutane daga yankunan da ake yakin, jami'an Majalisar Dinkin Duniya sun soma tattaunawa game da tura jami'an sa ido, domin tabbatar da an yi abin da ya kamata.

Akwai kyakkaywar fatan cewa kasashen da ke da rabuwar kawuna game da Syria, za su hada kai wajen cimma wata sabuwar yarjejeniya game da rikicin.