IMF: An samu Christine Lagarde da laifin sakaci

Asalin hoton, AFP
Christine Lagarde ta ce ta aikata lamarin ne da kyakkyawar niyya
Wata kotu ta samu shugabar Hukumar lamuni ta duniya IMF, Christine Lagarde da laifin sakaci, amma kuma kotun ta ce ba za a hukunta ta ba.
A shekarar 2008, lokacin tana matsayin Ministar Kudi, Misis Lagarde ta amince a bai wa wani dan kasuwa, Bernard Tapie, dala miliyan 429 kudin sayen wani kamfani.
Misis Lagarde dai ba ta halarci shari'ar da aka gudanar a birnin Paris ba, saboda ta tafi birnin Washington na Amurka daga Faransar.
Sai dai a yayin gudanar da shari'ar ranar Juma'a ta yi bayanin cewa ta aikata lamarin ne da kyakkyawar niyya.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayar da rahoton cewa Lauyanta ya ce za su kalubalanci hukuncin.
An gudanar da shari'ar Lagarde mai shekaru 60 ne, a kotun CJR, kan laifin babbar jami'ar da ta nuna halin sakaci a gwamanti.
Lagarde dai ta tsallake rijiya da baya, ganin idan da an kamata da laifin cin hanci maimakon nuna sakaci, da ta samu hukuncin shekara daya a gidan kaso.