Kasashe na alhini kan kisan Jakadan Rasha a Turkiyya

Asalin hoton, AP
Andrei Karlov na ziyartar wurin baje kolin kayan zane-zane ne a babban birnin kasar Turkiya
Shugabannin kasashe na ci gaba da bayyana alhininsu bisa kisan da aka yi wa Jakadan Rasha kasar a Turkiyya.
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin,ya bayyana kisan jakadan a matsayin takalar fada da aka kulla da nufin wargaza yunkurin kawo zaman lafiya a kasar Syria.
Shima a nasa bangaren shugaba Recep Tayyip Erdogan na kasar Turkiya ya bayyana lamarin da cewa tamkar hari ne ga kasar sa.
A cikin wata sanarwa zababben shugagan Amurka mai jiran gado Donald Trump, ya mika ta'aziyyarsa kan kisan jakadan na Rasha, inda ya ce wajibi ne kasashen duniya su yi alla-wadai da kisan.
Shi ma a sakon da ya aike ta hannun kakakinsa, sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya ya yi alla-wadai da kisan jakadan na Rashan yana mai cewa babu wata hujja ta kashe jami'in diplomasiyya ko kuma fararen hula, inda ya kuma yi fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata.
Shi dai Andrei Karlov na jawabi ne a wurin taron baje koli lokacin da maharin ya fara harbe-harbe yana ta kabbara tare da cewa kada a manta da Aleppo kada a manta da Syria.
Rahotanni sun ce maharin mai suna Mert Altintas - mai shekaru 22 dan sandan kasar Turkiyya ne, koda yake mahukunta sun ce ana ci gaba da gudanar da bincike.
An dai garzaya da Mista Karlov zuwa asibiti cikin gaggawa, inda daga bisani aka tabbatar da cewa ya mutu.
A kwanakin baya-bayan nan Rasha da Turkiyya sun yi aiki tare domin samar da yarjejeniyar tsagaita wuta a birnin Aleppo.