Daliban Firamari sun farantawa sojojin Najeriya

Daliban Firamari sun farantawa sojojin Najeriya

Asalin hoton, Nigerian Army

Bayanan hoto,

Daliban Firamari sun farantawa sojojin Najeriya

Wasu 'yan yara dalibai daga wata makaranta a Legas, sun gabatar wa da dakarun da ke yaki a rundunar da ake yi wa lakabi da lafiya dole, da kwalayen ababan more rayuwa a Maiduguri da ke jihar Borno.

Sanarwar da ta fito daga rundunar sojin Najeriya, ta ce kayayyakin da daliban makarantar Children International School watau CIS, da ke Lekki a jihar Legas, suka bayar gudunmuwa, sun hada da buroshi da man goge hakora da audugar mata, da aska, da cin gam da tawul-tawul da sabulan wanka da alawa da katin waya da katunan gaisuwa da kuma wasiku masu sosa rai, cikin kwalayen da aka rubuta "Ziploc" a jikin.

A lokacin mika kyaututtukan , jagoran 'yan makarantar, Bhila Kiphani, ya ce daliban ne da kan su suka bayar da gudunmuwar daga cikin kudin alawus din su na makaranta, domin dadadawa sojojin Najeriya, wadanda suke fadi tashi wajen ganin sun tsare kasar daga rikicin 'yan ta'adda.

A wasu daga cikin wasikun da daliban suka rubuto, akwai wadanda ke ma dakarun godiya da kokarin da suke yi na sanya murmushi a bakunan al'ummar Najeriya, wani kuma ya ce "Ina godiya da yakin da kake yi a madadina", wani kuma ya ce "Ina godiya da sadaukar da rayukarku da kuka yi mana," kuma wani ya ce, "Na gode soja, ina maka fatan ka koma gida lafiya."

Jagoran rundunar Lafiya Dole, Birgadiya Janar Victor Ezugwu

Asalin hoton, Nigerian Army

Bayanan hoto,

Jagoran rundunar Birgadiya Janar Victor Ezugwu ya ce kyauatar ta sosa masa zuciya

Jagoran rundunar Birgadiya Janar Victor Ezugwu ya yaba wa daliban wajen tunawa da sojojin Najeriya, a yayin da suke tsakiyar fada a cikin dajin Sambisa.

Ya ce, "Tun zuwa nan nan wannan shi ne yanayi da ya fi sosa min rai, ganin yadda yara da basu fi shekaru biyu uku ba, har su hada 'yan kudadensu, kuma su tuna da dakarun Najeriya."