Nigeria: Kwastam ta kama makaman yaƙi a Legas

Shugaban hukumar kwastan Kanar Hamid Ali mai ritaya

Asalin hoton, NIGERIA CUSTOMS

Bayanan hoto,

Hukumar ta sha kama irin wadannan makamai

Hukumar kwastam ta Najeriya ta ce ta kama wata kwantena dauke da makaman yaƙi da ake ƙokarin shigowa da su cikin ƙasar a tashar ruwa ta Tin Can Island a Legas.

Hukumar ta ce ta kwashe tsawon kwanaki tana gudanar da bincike kuma sakamakon sa ta gano manyan bindigogi biyu ƙirar Pump Action da dubban harsasai da sauran kayayyakin yaƙi.

Wani babban jami'in hukumar a Legas Bashir Yusuf ya ce an shigo da kwantaina ne daga Amurka, kuma an kama mutum daya da ake zargin yana da hannu a lamarin kuma tuni aka mika shi ga hukumar tsaron farin kaya wato SSS.

Wannan ne karo na biyar a 'yan shekarun nan da reshen hukumar mai kula da gabar teku ta Tin can Island a Legas ke kama makamai da ake ƙokarin shigowa da su cikin kasar.

Masu lura da al'amura na ganin irin wadannan makamai kan kasance a hannun kungiyoyi masu tayar da kayar baya kamar Boko Haram da mayakn Niger Delta.

Haka kuma akan yi amfani da su wurin rikice-rikicen kabilanci da addini da kasar ke fama da su.