Kwararru daga Rasha na bincike kan kisan jakadan Rasha a Turkiya

Andrey Karlov ranar Litinin

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Kwararru daga Rasha sun fara bincike kan kashe kashe jakadan Rasha a Turkiya

Wata tawagar kwararru daga Rasha ta isa kasar Turkiya da nufin gano yadda aka hallaka jakadan Rasha a Turkiya.

Wani dan sanda ne dai ya harbe Andrey Karlov ranar Litinin yayin da yake jawabi a wani wajen taron baje koli lokacin da maharin ya fara harbe-harbe yana ta kabbara tare da cewa kada a manta da Aleppo kada a manta da Syria.

Rahotanni sun ce maharin mai suna Mert Altintas - mai shekaru 22 dan sandan kasar Turkiyya ne, koda yake mahukunta sun ce ana ci gaba da gudanar da bincike.

An dai garzaya da Mista Karlov zuwa asibiti cikin gaggawa, inda daga bisani aka tabbatar da cewa ya mutu.

Da alama dan sandan yana nuna adawa ne da rawar da Rasha ke takawa a yakin da ake yi a birnin Aleppo na Syria.

An dai harbe dan sandan nan take.

To sai dai shugaban Rasha Vladmir Putin da takwaransa na Turkiya Racip Tayyip Erdogan sun ce harin ba zai raunata dangantaka tsakanin kasashen ba.

Ana sa ran manyan jami'an diplomasiyya na Rasha da Turkiya da Iran za su yi wani taro a Rasha da yammacin Talatar nan, inda za su jaddada hadin kai tsaninsu.