Nigeria: Gwamnan Cross River zai nada karin mataimaka 6,000

Ya ce zai iya biyansu albashi

Asalin hoton, Cross River Government

Bayanan hoto,

Gwamna Ben Ayade zai bai wa mutane 6000 mukamin siyasa

Gwamnan jihar Cross River a kudu maso kudancin Najeria, Ben Ayade, ya bayyana cewa zai nada karin mataimaka 6,000 a watan gobe.

Hakan zai zama kari a kan masu bada shawara da mataimaka 1,500 da gwamnan ke da su yanzu haka.

Jaridar Daily Trust ta rawaito gwamnan yana jawabi a Calabar babban birnin jihar, bayan kwanaki 10 bayan nasarar da ya samu a kotun koli a shari'ar da Barrista Joe Agi yake kalubalantar gwamnan kan zabensa.

A jawabin da ya yi wa dubban magoya bayansa a filin wasa dake Calabar, gwamna Ben ya ce manufar nade-naden ita ce tabbatar da cewa kowane bangare ya amfana da gwamnati, da kuma daukar matasa da suka kammala jami'a aiki.

Gwamanan ya ce kada jama'a su damu da yadda za a ringa biyan albashi ga mutanen 6,000 da za a dauka.

To sai dai wasu bayanai sun rawaito cewa a makon jiya wasu ma'aikatan kananan hukumomi da malaman sakandare sun yi zanga-zanga a ofishin gwamnan kan rashin biyansu albashin wata bakawai.