Jakadun Gambia sun bukaci Yahya Jammeh ya sauka

Shugaba Jammeh ya ce ba zai saukaba

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Jakadun Gambia sun bukaci Jammeh ya sauka

Jakadun Gambia 11 da ke aiki a kasashe daban daban sun yi kira ga shugaba Yahya Jammeh ya mika mulki ga Adama Barrow sannan ya yi masa murna.

Jakadun sun yi kiran ne a wani bangare na matsawa Yahya Jammeh lamba kan kalubalantar sakamakon zaben da ya sha kaye, bayan tun da farko ya taya wanda ya samu nasara Adama Barrow murna.

A wata wasika ta hadin gwiwa, jakadun sun yi kira ga shugaban na Gambia mai barin gado ya mutunta hukuncin da 'yan kasar suka yanke, sannan ya tabbatar da an mika mulki cikin kwanciyar hankali.

Kalaman sun fi kama da na diplomasiyya, maimakon na barazana.

Jakadun dai sun hada da na Amurka da China da Rasha da kuma na Birtaniya.

Kawo yanzu dai duk wani yunkuri da kungiyar ECOWAS ta yi na shawo kan Yahya Jammeh ya sauka daga mulki ya ci tura.