Nigeria: Ma'aikatan Arik sun jingine yajin aiki

Ma'aikatan Arik sun jingine yajin aiki

Asalin hoton, Arik Air

Bayanan hoto,

Kamfanin Arik ya cie an shawo kan matsalar

Kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Arik Air a Najeriya ya koma aiki kwana daya bayan yajin aiki da zanga-zangar da ma'aikatan kamfanin suka yi ranar Tala

Kamfanin ya koma aiki ne bayan an cimma wata yarjejeniya da ma'aikatan, wadanda ke nuna damuwa a kan rashin biyansu albashi har tsawon wata bakwai.

Yajin aikin dai ya hana fasinjoji da dama tafiye-tafiye a fadin kasar.

Shugaban kungiyar ma'aikatan Tokuboh Korodo ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa sun tattauna da shugabannin kamfanin, kuma sun amince za su biya ma'aikatan kudaden da suke binsu zuwa karshen watan nan.

Arik dai shi ne kamfanin jirgi mafi girma a Najeriya, to sai dai yana fuskantar matsaloli da dama da suka hada da karancin man jirgi, abin da ya sa ya rage yawan jiragensa da ke sufuri a kasar.ta.