Nigeria: An cimma yarjejeniyar zaman lafiya a Plateau

Asalin hoton, Platue government
Gwamnan jihar Platue Simon Lalung ya goyi bayan yarjejeniyar
Wasu al'umomi a jihar Plateau ta Najeriya sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da juna, domin kawo karshen tashe-tashen hankulan da suka shafe shekaru suna yi.
An saka hannun kan yarjejeniyar ne a wajen wani biki da aka gudanar a garin Shendam da ke kudancin jihar.
Bikin ya samu halartar jakadun kasashen Amurka da Jamus, da kuma gwamnan jihar ta Plateau Mista Simon Lalung.
Tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya Malam Nuhu Ribadu, shi ne ya jagoranci kulla wannan yarjejeniya karkashin kulawar wata kungiyar agaji ta duniya mai suna HD.
Ribadu ya shaida wa BBC cewa mabiya addinai mabanbanta da kuma kabilu sun bayyana cewa ya kamata a kawo karshen kashe-kashen da suka addabi yankin.
Ya kara da cewa al'ummomin sun dauki alkawarin babu mai kara tayar da fitina.
"Sarakunan gargajiya da dama sun halarci wajen, kuma gwamnatin jihar ta Platue ta yi alkawarin tabbatar da aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma," in ji Ribadu.
Malam Nuhu Ribadu ya ce za kuma a tuntubi gwamnatin tarayya domin ita ma ta taka rawar da ta kamata wajen tabatar da zaman lafiyar.
A yayin yarjejeniyar dai al'ummomin sun ce sun yafe duk wani abu da aka yi musu.
Gwamnatin jihar Platue dai ta kafa wata hukuma ta zaman lafiya da za ta ringa daukar matakan hana faruwar rikice-rikice.