Iwan Roberts: Fifa ba ta da sauran kima

'Yan wasa sun yi layi yayin da 'yan kallo suka hadu domin nuna alamar tunawa da 'yan mazan jiyan

Asalin hoton, HUW EVANS AGENCY

Bayanan hoto,

Tunawa da 'yan mazan jiyan Birtaniya kafin fara wasan Wales da Serbia na neman zuwa gasar kofin duniya ta 2018

Tsohon dan wasan Wales Iwan Roberts ya ce tarar da Fifa ta ci yankuna hudu na tarayyar Birtaniya kan amfani da 'yan wasansu suka yi da alamar tunawa da sojinta da suka mutu a yakin duniya na daya abin takaici ne.

Robert ya ce: ''Wannan abin da Fifa ta yi abin mamaki ne da takaici, amma ka san me? Ban yi mamaki ba domin hukuma ce ta shirme kawai

Tsohon dan wasan na Wales, ya kara da cewa : ''Ka ci tarar yankuna hudu saboda martaba mutanenmu da suka rasa ransu a yake-yaken duniya abu ne mai tayar da hankali ma.''

Ya ce : ''Na san muna karkashin dokoki ne amma ina ganin shirme ne kawai abin da Fifa ta yi, kuma ina fatan Wales za ta yi koyi da Ingila ta daukaka kara.''

Roberts, wanda ya buga wa Wales wasa 15, ya ce daman tuni martabar hukumar kwallon kafar ta duniya ta zube.

Kuma masu sha'awar wasan kwallon kafa ba sa ganin kimarta.

Hukumar ta ci tarar Ingila da Wales da Scotland da kuma Ireland ta Arewa kan wasanninsu na neman zuwa gasar kofin duniya a watan Nuwamba.

'Yan wasan Ingila da na Scotland sun daura bakin kyalle mai alamar jan fure wanda shi ne alamar tunawa da 'yan mazan jiyan.

Su kuwa Wales da Ireland ta Arewa sun yi holin alamar ne a fili da kuma kan benen 'yan kallo domin tunawa da ranar wadda ta zo daidai da lokacin wasannin.

Hukumar kwallon kafar ta duniya ta dauki amfani da alamar ta tunawa da 'yan mazan jiyan na Birtaniya a matsayin alama ta siyasa.

Kuma dokokinta sun hana amfani da wata alama ta siyasa ko addini ko wani abu na bangaranci ko wata fafutuka a wasanninta.

Fifa ta ci tarar Scotland da Wales su duka biyun fan 15,694, Irelant ta Arewa kuwa za ta biya fan 11,770.

Ita kuwa hukumar kwallon kafa ta Ingila ta ce za ta daukaka kara ne a kan tarar da Fifar ta yi mata ta fan 35,311.

Su kuwa hukumomin Wales da Scotland da Ireland ta Arewa har yanzu ba su yanke shawara kan matakin da za su dauka ba.