Kungiyoyi na sha'awar Saido Berahino

Saido Berahino na nuna damuwa kan yadda West Brom take kin ba shi damar tafiya wata kungiyar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Saido Berahino ya koma West Brom tun yana shekara 11

Dan wasan West Brom Saido Berahino ya samun goron gayyata daga wasu kungiyoyin Ingila da na wasu kasashen yayin da akae shirin bude kasuwar saye da sayar da 'yan wasa.

Berahino, mai shekara 23, ya dawo kungiyar ne bayan da ta tura shi wani sansani a Faransa domin ya samu damar rage kiba, kuma ya farfado da wasansa.

A ranar Litinin ya yi wa 'yan wasan kungiyar 'yan kasa da shekara 23 wasa a haduwarsu da Brighton, wanda shi ne wasansa na biyu da karamar kungiyar tun da ya dawo.

A karshen kakar bana kwantiragin Berahino zai kare da kungiyar ta West Brom.

Daga ranar 1 ga watan Janairu zai iya kulla takaitacciyar yarjejeniya ta kafin kwantiragi da wata kungiya wadda ba ta Ingila ba, wanda hakan zai ba shi damar tafiya ba tare da an biya wani kudi ba.

Amma kuma idan wata kungiya ce ta Ingila za ta dauke shi to a nan kuma kotu ce za ta yanke hukunci kan kudin da kungiyar ta dauke shi za ta biya West Brom a kansa.

Irin halin da Danny Ings ya samu kansa a ciki kenan lokacin da ya koma Liverpool daga Burnley a 2015, inda Liverpool din za ta iya kaiwa ga biyan fan miliyan 8 a kan Ings, wanda wannan shi ne kudi mafi yawa da kotu ta sa a biya.

Rabon da Berahino ya buga wa West Brom wasa tun 10 ga watan Satumba, kuma kwallon da ya jefa a ragar Chelsea ranar 27 ga watan Fabrairu ita ce ta karshe da ya ci.

Dan wasan haifaffen Burundi ya nuna matukar bacin ransa bayan da aka hana shi damar komawa Tottenham, wadda ta taya shi sau uku, ciki har da wanda ta saye shi fan miliyan 22 da rabi a 2015.

A bazarar da ta wuce West Brom ta ki amsa tayin da Stoke da Crystal Palace suka yi wa dan wasan na fan miliyan 20.