Berlin: Babu tabbacin an kama maharin da ya kashe mutane 12

Babu tabbacin an kama maharin da ya kashe mutane 12

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Motar ta afkawa masu sayayya a kasuwar Kirismeti da ke Berlin a kasar Jamus

Hukumomi a Jamus, sun ce ba zasu iya bayar da tabbacin cewa mutumin da aka kama a ranar Litinin shi ne direban babbar motar da ta afkawa kasuwar kirismeti a birnin Berlin.

Mutane goma sha biyu ne suka rasa rayukansu a lokacin da babbar motar ta afkawa kasuwar.

A wani taron manema labarai, shugaban 'yan sanda a Berlin, Klaus Kandt, ya ce kawo yanzu masu bincike ba su tabbatar ko mutumin da ake tsare da shi, shi ne ya kai harin ba.

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel, ta bayana harin a matsayin babban laifi.

Merkel ta ce za a yi nazari kan lamarin, kuma za a hukunta wadanda suka aikata wannan aika-aika kamar yadda dokokin kasa suka tanada.