Yarinya ta mutu saboda tana jinin haila

Al'ummar kauyen Gajra da ke gundumar Achham, wanda ke da nisan mil 275 daga Kathmandu

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Ana kebe mata masu jini haila da jini biki a kauyen saboda a cewarsu, ba su da tsafta

'Yan sanda a Nepal, na binciken mutuwar wata yarinya 'yar shekara 15, wacce aka kebe a cikin wata 'yar bukka mara iska, domin tana jinin haila.

Mutanen garin sun ce ta mutu ne sanadiyyar hayaki mai guba da ta shaka bayan da ta kunna wuta a dan dakin, domin jin dumi.

Wata tsohuwar al'adar addinin Hindu da ake cewa 'chhaupadi', ya tanadi cewa matan da ke jinin haila, da kuma wadanda ke jinin biki, basu da tsafta.

Gwamnatin Nepal dai ta haramta al'adar a shekarar 2005, amma kuma har yanzu ana ci gaba da ita a wasu kauyuka da ke yammacin kasar.

Mahaifin yarinyar mai suna Roshani Tiruwa ne ya gano gawarta a karshen makon da ya gabata, cikin bukkar da aka gina da duwatsu da laka a kauyen Gajra da ke gundumar Achham, wanda ke da nisan mil 275 daga Kathmandu.

Wasu al'umma da ke karkarar sun yarda cewa wani bala'i zai tasan masu idan basu kebe matar da ke jinin haila ba.

A yayin da kuma suke kebe, ba a basu isasshen abinci kuma a haramta masu shan madara.

Yawancin lokuta kuma bukkokin da ake kebe matan a ciki, suna zama ne da dabbobi, cikin kazanta, kuma a waje mai nisa daga muhallansu.

Masu suka dai sun ce gwamnatin kasar bata yi abun da ya kamata ba wajen ganin an haramta wannan al'ada, sun kuma ce tana tafiyar hawainiya wajen hana auren wuri a kasar.

Hukumomin kasar dai sun ce yana da wuya rana daya a sauya al'adar da ta riga zama jiki tsakanin al'umma.