An saki Musulmin da ake zargi da kisan mota na Berlin

Kasuwar kayan Kirismeti da ke Berlin

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

An rufe kasuwanin Kirismeti a birnin Berlin domin nuna alhini ga mutane da aka kashe

Masu shigar da kara a Jamus sun ce an saki dan Pakistan din da aka kama dangane da kisan da wata mota ta yi a kasuwar Berlin.

Gwamnatin Jamus ta ce za a rufe kasuwanin Kirismeti a birnin Berlin domin nuna alhini ga mutane da aka kashe.

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel, ta ce lamarin zai yi matukar ciwo idan aka gano cewa wanda ya kai harin dan gudun hijira ne.

Merkel dai ta nemi 'yan kasar da kar su bari lamarin ya sa su shiga wani yanayi na fargaba.

Ta kuma sha alwashin hukunta wadanda ke da hannu a cikin lamarin.